Mr.Eaton wanda yake kan ziyarar yini uku a kasar Zimbabwe ya fada a wata tashar rediyon kasar cewa, matsalar sayen wasanni yana cigaba da karuwa a duniya, a don haka ya zama wajibi gwamnatoci na kasashen duniya su bayar da himma wajen ganin an kawar da wannan dabi`a daga wasannin kwallon kafa.
Ana sa ran Mr. Eaton zai nazarci rahoton da kwamitin bincike na hukumar wasannin kwallon kafa na Zimbabwe ZIFA ya gudanar domin hada shi da na hukumar FIFA.
A yanzu haka dai hukumar ta FIFA tana gudanar da bincike a kan wasu kasashe 25 bisa zargin aikata cacar wasanni.
Wannan al`amari dai ya kasance sabon abu a kasar Zimbabwe bayan abun kunyar da ya auku na Asiagate inda ake zargin kasar ta Zimbabwe da hannun wajen kulla murda-murdar wasanni a yayin wani ziyara zuwa yankin gabashin.(BAGWAI)