Wannan shi ne matsayi mafi koma baya da kungiyar kwallon kafa ta Bafana Bafana ta kasar Afirka ta Kudu ta samu kanta, kuma wannan shi ne karo na farko da kungiyar ta fita daga cikin jerin kasashe 50 da ke kan gaba tun daga watan Janairu na shekarar bana.
Sakamakon ya nuna cewa, Afrika ta Kudu ta yi kasa da mataki 2 zuwa ta 9 a nahiyar Afrika.
A watan Mayu, kungiyar Bafana ta taba kaiwa matsayi na 38 wanda shi ne babban mataki da ta kai a cikin shekaru 7 da suka gabata, bayan da ta yi nasara a kan takwarorinta na Kenya, Masar, da Tanzania.
Duk da kunnen doki da suka yi da Masar a birnin Alkahira, kana ta doke kasar Burkina Faso da ci uku da nema a wasan da aka yi a birnin Johannesburg, amma ta koma baya sakamakon rashin tabuka wani abin a zo a gani a bangaren wasanni.
A gasar share fagen cin kofin kwallon kafa na Afirka, kasar Niger ta doke ta da ci biyu da daya a Niamey a farkon watan nan, abin da ya sa Afirka ta Kudu ta koma baya a jerin sunayen kasashen duniya a fagen kallon kafa. (Salamatu)