A lokacin da yake ganawa da `yan wasan na kungiyar Meteors da kuma kungiyar `yan wasan rukunin mata Black Princesses a ranar Alhamis din nan da ta gabata, mataimakin shugaban kasar ta Ghana ya ce, gwamnatin kasar tuni ta umarci ma`aikatar matasa da wasanni da ta gaggauta biyan su ragowar hakkokin da suke bi.
Gwamnatin kasar Ghana dai ta tabbatar da cewa zuwa karshen wannan watan za ta shirya bikin bayar da kyautuka ga dukkan `yan wasan da suka samu lambobin yabo yayin gasar wasannin.
Kungiyar kwallon kafa ta Black Metors wadda ta kunshi `yan wasa na gida ta samarwa kasar Ghana lambar zinare a yayin gasar wasanni na Maputo bayan da ta lallasa kasar Afrika ta Kudu da ci hudu da biyu a bugun daga kai sai mai tsaron gida yayin karawar karshe.
Ita kuwa kungiyar kwallon kafa ta mata ta kasar ta Ghana Black Princesses ta ciyowa kasar lambar azurfa bayan da ta doke kasar Cameroom da ci daya da nema a gasar karshe.(BAGWAI)