Za dai a karkare wasannin da zasu fidda zakara a wannan gasa ne daga ranar 10 ga watan Janairun shekara mai zuwa, zuwa 1 ga watan Fabrairun wannan shekara a kasar Afirka ta Kudu.
Wannan dai gasa da aka kaddamar a karon farko cikin watan Satumbar shekarar 2007, karkashin kulawar hukumar gudanar da wasanni ta CAF, an fara bugata ne a shekarar 2009, tsakanin kulaflikan kasahsen Afrika mafiya kwazo dake da 'yan wasa na gida zalla. Janhuriyar Dimokaradiyyar Congo ce dai ta fara lashe kofin gasar wadda Côte d'Ivoire ta dauki bakunci a wannan shekara. A karo na biyu kuwa an gabatar da gasar ne a kasar Sudan cikin shekarar 2011, inda a wannan lokaci kasar Tunisia ta dauki kofin. Ana kuma ci gaba da gudanar da gasar bayan shekaru Biyu-Biyu, wadanda suke sabawa shekarun gasar cin kofin nahiyar Afrika wato CAF. Inda yayin da gasar ta CHAN ta gaba zata gudana a shekara mai zuwa, ita kuwa gasar cin kofin nahiyar Afrka CAN ta gaba, na tafe ne cikin shekarar 2015 mai zuwa.
Hukumar CAF dake shirya gasar, na fatan hakan zai karfafa kwazon 'yan wasan gida, ya kuma basu damar haskakawa a idon duniya a nan gaba. (Saminu)