Kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ta Najeriya za ta ci gaba da horo a sansanin dake garin Calabar ranar 10 ga watan Maris kafin karawa da za ta yi da kasar Kenya a wasan fidda masu zuwa gasar cin kofin duniya wadda za'a yi a kasar Brazil a shekarar 2014.
Zakarun na Afirka su ne ke saman teburin kungigoyin rukunin H bayan wasanni biyu da suka buga inda suka samu maki 4.
Wadanda ke biye da su su ne 'yan wasan Namibia da maki uku, sai kuma Malawi mai maki biyu, kana Kenya na da maki daya tal.
Mai magana da yawun kungiyar ta Super Eagles Ben Alaiya yayin da yake jawabi ga manema labarai a garin Abeokuta ranar Alhamis ya ce, tarayyar kungiyoyin kwallon kafa ta Najeriya (NFF) za ta ba da cikakken hadin kai ga shirye-shiryen masu koyar da 'yan wasan karkashin Stephen Keshi.
Ya musanta rahotanni dake cewar, akwai rashin jituwa tsakanin masu koyar da 'yan wasan da hukumar ta NFF, inda ya ce, rahotanin karya ne kawai na marubuta wadannan labarai.(Lami)