in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za'a shirya wasan kwallon kafar sada zumunci tsakanin jamhuriyar demokaradiyar Congo da kasar Angola
2011-08-23 10:31:25 cri

'Yan wasan kwallon kafa na "Leopards football A" da kuma 'yan wasa matasa za su kara a ranar Asabar da takwarorinsu na kasar Angola bi da bi da 'yan wasan "Lunda Notre" da na Luanda dake cikin tsarin gasar sada zumunci, in ji shugaban kungiyar kwallon kafa ta kasar Angola FECOFA, mista Constant Omani a ranar Litinin.

Za'a shirya wannan wasa albarkacin zagayowar ranar haifuwar shugaban kasar Angola Eduardo dos Santos, kuma wasar tana da manufar kara karfafa dankon zumunci tsakanin kasashen biyu, mista Omani ya kara da cewa.

Haka kuma shugaban kungiyar FECOFA ya nuna cewa wadannan wasanni biyu wata dama ce ga 'yan kwallon Leopards na RDC kara kwarewarsu domin shirya wasanninsu na gaba da za su kara bi da bi da 'yan wasan "Lions de la Teranga" na kasar Senegal a ranar 3 ga watan Satumbar shekarar 2011 a filin kwallon kafa na "Amitie" dake birnin Dakar, dake cikin rana ta biyar da kuma yinin karshe na rukunin 5, a gasar tankade da rairaiyi ta cin kofin nahiyar Afrika karo ta 28 da kasashen Gabon da Guinea Equatoriale za su shirya tare a cikin watan Febrairun shekarar 2012.

'Yan wasan "Daring Club Motema Pembe" (DCMP) ba za su halarci wadannan wasannin ba ganin sun shiga gasannin Afrika. Kuma 'yan wasan na DCMP za su kara a ranar 27 ga watan Agusta tare da 'yan matasan Kabylie a cikin wasanin rana ta hudu na rukunonin cin kofin kungiyar kwallon kafa ta nahiyar Afrika wato CAF. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China