Firaministan Palasdinu Rami Hamdallah wanda ke ziyara a kasar Lebanon, ya bayyana a ran 28 ga wata a birnin Beirut cewa, shawarari tsakanin Palasdinu da Isra'ila da aka farfado da su a watan Yulin da ya gabata, ko alama ba su haifar da wani ci gaba ba. Ya ce bangarorin biyu ba su kai ga cimma matsaya daya ba, kan wasu manyan batutuwa ciki hadda batun 'yan gudun hijira, da na shata kan iyakar kasa, da batun masu aikata laifufuka da aka tsarewa a kurkuku, da batun albarkatun ruwa da kuma matsayin birnin Kudus.
Bisa labarin da kafar yada labaru ta kasar Lebanon ta bayar an ce, Rami Hamdallah ya gana da firaministan gwamnatin wucin gadin kasar ta Lebanon, inda suka tattauna kan halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya, da dangantakar dake tsakanin Palasdinu da Isra'ila da dai sauran batutuwa.
Yayin taron manema labaru da aka yi bayan ganawar, Hamdallah ya bayyana cewa, Palasdinu za ta ci gaba da nacewa matsayin warware rikicin dake tsakanin bangarorin biyu, ta hanyar tabbatar da kafuwar kasashen Palasdinu da Isra'ila, yana mai fatan za a samu daidaito bayan shawarwarin.
Haka zalika Hamdallah ya yi kira ga wasu kasashe dake goyon bayan shawarwarin da ake yi ciki hadda Amurka, da su yi iyakacin kokarin taimakawa Palasdinawa ta fuskar kare hakkinta, ta hanyar kafa kasar Palasdinawa mai hedkwata a birnin Kudus, bisa shatin iyakar kasar ta shekarar 1967.
Game da matsugunan Yahudawa da Isra'ila ke ginawa a fiyalen Palasdinu kuwa, Hamdallah ya bayyana cewa, gwamnatinsa za ta ci gaba da aiwatar da manufofin kiyaye hakkin Palasdinawa, tare da kare zamantakewarsu, da ikon mallakar filayensu yadda ya kamata. (Amina)