Ranar Laraba 27 ga wata a birnin Ramallah dake yammacin gabar kogin Jordan, shugaban hukumar al'ummar Palasdinawa Mahmoud Abbas ya jaddada cewa, a watan Satumba na shekarar bana, zai nemi taron MDD da al'ummar duniya dasu amince da kasar Palasdinu da aka kafa kan iyakar Palasdinu da Isra'ila a shekarar 1967 kafin yakin yankin gabas ta tsakiya.
Mahmoud Abbas ya jaddada cewa, gabatar wa MDD wannan batu bai saba da shawarwarin tsakanin bangarorin biyu ba. Ya ce, yanzu shawarwarin da suke yi yana fuskantar mawuyacin hali saboda gwamnatin Isra'ila ta ki amincewa da dakatar da matsugunan Yahudawa da layin iyakar da aka kafa kafin yakin shekarar 1967. Bangarorin hudu da abin ya shafa wato MDD, EU, Amurka da Rasha ba su cimma ra'ayi daya ba kan batun farfado da shawarwari a tsakiyar wannan wata, hakan ya sa, Palasdinu take neman taimako daga kasashen duniya. A gun taron, Mahmoud Abbas ya yi kira ga jama'ar Palasdinu da su matsa lamba kan kasashen duniya domin neman samun taimako.
Ya zuwa yanzu, hukumar tana dauke da dabaru sosai domin yin amfani da hanyar diplomasiyya cikin babban taron MDD.(Amina)