A ran 18 ga wata, a yayin da sarkin kasar Jordan Abdullah ke ganawa da manzon musamman da ke lura da batun gabas ta tsakiya, kuma tsohon firaministan Birtaniya Tony Blair wanda ya kai ziyara a Amman, babban birnin kasar, sarki Abdullah ya jadadda cewa, ya kamata kasa da kasa sun ci gaba da sanya kokarin tsayar da matakan cin zali da Isra'ila take dauka kan yankin Gaza, ta yadda za a iya hana tsanancewar halin da wurin ke ciki. Ya kuma nuna cewa, tabarbarewar halin da ke kasashen Palesdinu da Isra'ila ke ciki zai kawo illa ga kokarin da aka yi wajen inganta yunkurin zaman lafiya a gabas ta tsakiya, a sa'i daya kuma zai kawo matukar barazana ga halin tsaro da na karko a shiyyar. Ya yi gargadi cewa, matakan cin zalin da Isra'ila ta dauka kan yankin Gaza za su haddasa wahaloli ga zaman rayuwar mazaunan wurin wadanda suka riga cikin mayuyacin hali a zirin Gaza.
Daga bisani kuma, a ran 18 ga wata, shugaban kasar Faransa Hollande ya yi shawarwari da shugaban kasar Masar Mohamed Morsi ta wayar tarho, inda suka sake tattaunawa kan tabarbarewar rikici tsakanin Palesdiu da Isra'ila. A wannan rana, fadar shugaban kasar Faransa ta ba da wani rahoto, inda ta bayyana cewa, shugabannin kasashen biyu sun yi tattaunawa kan rikicin na zirin Gaza, kuma suna fatan nan da nan kasashen Falesdinu da Isra'ila za su iyar cimma wata yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakaninsu. (Maryam)