Babban sakataren MDD Ban Ki-Moon ya yi kira ga Palasdinu da Isra'ila a ran 5 ga wata cewa, ya kamata, bangarorin biyu su yi shawarwari tun da wuri, domin ya zamo wani matakin warware rikicin dake tsakaninsu yadda ya kamata.
A gun taron kwamitin tabbatar da ikon Palasdinawa da MDD ta yi a wannan rana, Ban Ki-Moon ya ba da jawabi cewa, MDD ta baiwa Palasdinu matsayin 'yar kallo a MDD daga watan Nuwamba na shekarar bara, kuma yin hakan ya ba da muhimmanci sosai ga warware rikicin nasu a kan kari.
Ya ce, hanya daya tilo ta daidaita wannan batu ita ce yin shawarwari, tare Kuma da nuna fatan cewar sabuwar gwamnatin kasar Isra'ila za ta yi kokarin shiga wannan aiki na neman zaman lafiya da kuma sulhu da Palasdinu ta hanyar yin shawarwari.
Ban da haka, Ban Ki-Moon ya nuna rashin jin dadinsa matuka dangane da gina karin matsugunan Yahudawa da Isra'ila ta yi kwanan baya. Ya ce, wannan zai kawo cikas ga warware matsala dake tsakanin bangarorin biyu, don haka tilas a dakatar da gine-ginen.
Ya ce ya kamata bangarorin biyu su gudanar da kudurorin kwamitin sulhu na MDD da kuma cika alkawarin da suka yi na warware rikicin nasu ta hanyar yin shawarwari da kuma daidaita wasu manyan batutuwa, ciki hadda tabbatar da yankin kasa, tsaron kasa, birnin kudus, 'yan gudun hijira, matsuguna, albarkatun ruwa da dai sauransu. (Amina)