in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Palasdinu ta tabbatar da mika bukatar ta na neman zama kasa 'yar kallo ta MDD
2012-11-28 10:15:54 cri
Ranar 27 ga wata, zaunannen dan kallo na Palasdinu dake MDD Riyad Mansour ya yi hasashe a birnin New York, inda hedkwatar MDD take cewa, shugaban hukumar al'ummar Falesdinu PNA Mahmoud Abbas zai gabatar da rokonsu ga babban taron MDD na neman zama kasa 'yar kallo a MDD a ran 29 ga wata, wanda ya kasance muhimmin lokaci ne ga MDD da Palasdinu.

Yayin taron manema labarai a wannan rana da safe, Mansour ya ce, mai yiwuwa ne, a yayin babban taron na MDD da za'a yi a ran 29 ga watan za a amince da Palasdinu da ta kasance tamkar wata kasa a duniya.

Za a tabbatar da matsaya daya na duniya na warware rikicin dake tsakanin Palasdinu da Isra'ila ta hanyar tabbatar da matsayin wadannan kasashen biyu a babban taron, wanda kuma zai samar da kyakyawan sharadi wajen yin shawarwari tsakaninsu, ta yadda za a kawo karshen yanayin da wata kasa ta mamaye yankin wata kasa ta daban.

Mansour ya jaddada cewa, ya kamata, bangarori daban-daban su mutunta matsayin Palasdinu da zarar kasashen duniya sun tabbatar da matsayin kasar Palasdinu. Ya ce, bayan ranar 29 ga wata, Palasdinu na fatan samar da yanayi mai kyau wajen cimma matsaya daya da Isra'ila tare kuma da fatan su zauna tare cikin lumana. (Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China