Essam Haddad ya ce, Masar za ta yi iyakacin kokari wajen ciyar da ayyukan cimma burin tsagaita bude wuta tsakanin bangarorin biyu gaba, ta yadda za a iya samun zaman lafiya da kyakkyawan yanayi a yankin. Ya kara da cewa, a halin yanzu, Masar tana tattaunawa tare da Isra'ila da 'yan kungiyar Hamas, domin cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta, kuma bangarorin biyu suka fidda bukatunsu kan tsayar da musayar wuta, kuma sun gane muhimmancin tsayar da musayar wuta sosai. Essam Haddad ya kara da cewa, shugaban kasar Masar Morsi ya riga ya tattauna da shugaban kasar Amurka Obama kan rikici tsakanin Falesdinu da Isra'ila ta wayar tarho, inda ya bayyana cewa, kasar Amurka ta kasance kasar da ta fi kawo tasiri ga Isra'ila.(Maryam)