in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AL ta kira taron musamman dangane da batun Palesdinu da Isra'ila
2012-11-18 17:11:52 cri
Ranar Asabar 17 ga wata, kungiyar kawancen kasashen Larabawa wato AL ta shirya taron musamman na ministocin harkokin waje a babban zaurenta da ke birnin Alkahira, babban birnin kasar Masar, inda aka tattauna batun Palesdinu da Isra'ila.

Bayan taron, Nabil el-Araby, babban sakataren kungiyar AL ya bayyana wa manema labaru cewa, a yayin taron, an tsai da kudurin kafa wata tawagar ministoci a karkashin shugabancinsa, wadda za ta kai ziyara zirin Gaza a 'yan kwanaki masu zuwa, da zummar mara wa mazauna wurin baya. Tawagar za ta bude kofa ga kowa da kowa, ministocin harkokin waje na dukkan kasashe mambobin kungiyar za su gabatar da rokonsu na zuwa zirin Gaza.

Sa'an nan kuma, an yanke shawarar bai wa kwamitin kula da shirin wanzar da zaman lafiya na kasashen Larabawa da ke karkashin shugabancin AL iznin sake kimanta matsayin da kasashen Larabawa za su tsaya a kai yayin da aka dakatar da aikin shimfida zaman lafiya a tsakanin Palesdinu da Isra'ila, da sakamakon da aka samu wajen aiwatar da shirin wanzar da zaman lafiya na kasashen Larabawa, wanda kasashen Larabawa suka mayar da shi tamkar wasu muhimman tsare-tsare, da kuma amfanin tsarin yin tattaunawa a tsakanin MDD, Amurka, kungiyar tarayyar Turai da Rasha.

Har wa yau kuma, taron ya nuna wa kwamitin sulhu na MDD rashin jin dadinsa, saboda ba ta dauki wajababbun matakai na hana Isra'ila ta kutsa kai cikin zirin Gaza da yi wa shugabannin Palesdinu kisan gilla ba. Ya kuma yi kira ga kwamitin da ya sauke nauyin da ke kansa na wanzar da kwanciyar hankali da zaman lafiya a duniya, wanda aka tanada cikin kundin tsarin MDD.

An labarta cewa, hukumar kiwon lafiya ta zirin Gaza ta furta cewa, a ranar 17 ga wata, jiragen saman yaki na Isra'ila sun ci gaba da kai hari a zirin Gaza, inda Palasdinawa 10 suka rasa rayukansu. Kawo yanzu Palasdinawa 40 sun halaka sakamakon hare-haren yayin da wasu 350 ko fiye suka jikkata.

A wata sabuwa kuma, wani jami'in kungiyar Hamas, wanda ba ya so a ambata sunansa, ya bayyana a ranar 17 ga wata cewa, shugabannin kungiyar sun gabatar da sharadi na cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta tare da Isra'ila. Kungiyar ta bukaci Isra'ila ta sanya hannu kan yarjejeniya tare da ita a rubuce a karkashin sa idon kasashen duniya. Amma sharadi na farko shi ne Isra'ila ta soke takunkumin da take sanya wa zirin Gaza tun bayan shekarar 2007, sa'an nan ba za ta sake kafa shinge kan bunkasa zirin ba, kuma ba za ta ci gaba da yi wa shugabannin kungiyar Hamas kisan gilla ba. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China