Kasar Isra'ila za ta saki kashi na biyu na Palasdinawa da take tsare daga ranar 29 ga wata a daf da wayewar garin ranar Laraba ranar 30 ga wata, gwamnatin Palasdinu za ta shirya shagulgula, amma shawarar da aka yanke ta sakin Palasdinawan ta haddasa bambancin ra'ayoyi a bangaren Isra'ila.
A wannan karo, za a saki Palasdinawa da yawansu zai kai 26, inda 21 daga cikinsu za su koma gidajensu da ke yammacin gabar kogin Jordan, a yayin da sauran palasdinawa 5 za su koma yankin Gaza. Bisa labarin da muka samu, an ce, yawancin Palasdinawan da za a sako a rukuni na biyu an fara tsare su ne kafin a daddale yarjejeniyar Oslo a shekarar 1994.
Shugaban Palesdinu Mahmoud Abbas ya bayyana cewa, za a kara sa kaimi ga Isra'ila da ta saki dukkan Palasdinawa da take tsare da su.(Danladi)