Ranar 20 ga wata, rikicin daya barke tsakanin Palasdinu da Isra'ila ya kara tsananta. Bisa labarin da hukumar ba da jiyya ta yankin Gaza ta bayar, an ce, matakin soja da Isra'ila ta dauka na tsawon mako daya ya yi sanadiyyar mutuwar Palasdinawa 130 yayin da wasu fiye da dubu suka raunana. An ce, kungiyar Hamas da kungiyar Jihad ta Palasdinu sun kai harin rokoki a kalla 1700 kan Isra'ila, abin da ya yi sanadin mutuwar 'yan Isra'ila 5.
Game da rikici wanda ya kara tsananta a tsakanin bangarorin biyu, kasashen duniya na kokarin shiga tsakani, kuma sun yi kira ga bangarorin biyu da su tsagaita bude wuta nan take. Sakatariyar harkokin waje ta kasar Amurka Hillary Clinton ta isa birnin Jerusalem a wannan rana domin yin shiga tsakani, inda ce, Amurka na fatan ganin bangarorin biyu da su kulla wata yarjejeniya na lokaci mai tsawo wanda zai hana jin karar makamai saboda hakan zai biya bukatun bangarorin biyu tare da taimaka musu wajen kiyaye zaman karko a yankin gabas ta tsakiya.
An ce, a wannan rana kuma, babban sakataren MDD Ban Ki-Moom wanda shima ya kai ziyara a birnin Jerusalem ya nuna matukar rashin jin dadin sa kan harin da ake kaiwa, kuma ya yi kira ga sojojin Isra'ila da su magance yin amfani da karfin tuwo.
Ranar 19 ga wata, ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jiechi ya bugawa takwaransa na kasar Masar Mohammed Kamel Amr waya, inda suka yi musayar ra'ayi kan halin da ake ciki yanzu a zirin Gaza, kuma a nasa bayanin mista Yang ya ce, ba za a yarda da yin amfani da karfin tuwo yadda aka ga dama ba wanda zai haddasa asarar rayukan fararen hula.
Sin ta bayyana matsayin da ta dauka kan wannan batu sosai, kuma Sin ta kalubalanci bangarori daban-daban da wannan batu ya shafa da su amsa kiran da kasashen duniya suka yi, tare da dakatar da daukan matakin soja nan take. (Amina)