Sabili da haka, aka bukaci Isra'ila da ta dakatar da dukkan ayyukan da suka shafi kafa matsugunai, tare da janye dukkan mazaunan wurin ba tare da bata lokaci ba.
Rahoton na cewa, bisa sashe na 49 na yarjejeniyar Geneva ta hudu, dole ne Isra'ila ta dakatar da duk ayyukanta dangane da matsugunai ba tare da wani sharadi ba.
A sa'i daya kuma, rahoton ya bukaci Isra'ila da ta tabbatar da biyan kudin diyya yadda ya kamata domin sakayya kan hasarar 'yan Palestinu da aka keta hakkinsu da sauri.
A kuma wannan rana, ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila ta ba da wata sanarwa, inda ta mai da martani cewa, wannan rahoto ba shi da amfani ko kadan, kuma a ganinta, majalisar kare hakkin bil'adama tana nuna bambanci ga Isra'ila.
Bugu da kari, ma'aikatar harkokin waje ta Isra'ila ta bayyana cewa, dukkan ayyukan da za a yi, wato kamar irin wannan rahoto, za su kawo cikas ga kokarin tsara shirin daidaita rikici tsakanin Isra'ila da Palestinu cikin dogon lokaci.(Fatima)