in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sin ya yi kira ga Isra'ila da ta bunkasa shawarwari da Falesdinu
2012-12-20 14:17:02 cri
A ran 19 ga wata, zaunanen mataimakin wakilin kasar Sin da ke MDD Wang Min, ya bayyana a hedkwatar MDD da ke birnin New York cewa, Sin ba za ta goyi bayan Isra'ila kan gina matsugunan Yahudawa ba, kuma Sin na ci gaba da kira ga Isra'ila da ta dauki matakan ciyar da shawarwarin da ke tsakaninta da Falesdinu gaba, bugu da kari, ya kamata gamayar kasashen duniya su dukufa wajen bunkasa shawarwarin da ke tsakanin bangarorin biyu.

A wannan rana, an gudanar da wata tattaunawar sirri kan yanayin gabas ta tsakiya a kwamitin sulhu na MDD. Bayan tattaunawar, Wang Min ya bayyana cewa, kamar yadda ta saba, kasar Sin ba za ta amince da Isra'ila ta gina sabbin matsugunan Yahudawa a gabashin birnin Jerusalem, da yammacin kogin Jordan, da dai sauran yankunan da Isra'ila ta kwace daga bangaren Felesdinu ba.

Batun Falesdinu dai na cikin batutuwa na kan gaba, cikin dukkan matsalolin da yankunan gabas ta tsakiya ke fama da su,wanda ke jan hankulan al'umma a dukkanin fadin duniya, shi ya sa a cewarsa, za a iya samun kwanciyar hankali mai dorewa ne kawai a wannan yanki, idan aka warware matsalar Falesdinu yadda ya kamata.

Wang Min ya kara da cewa, bangaren Sin na fatan bangarorin da abin ya shafa za su nuna goyon bayansu ga shirye-shiryen da MDD ta tsara, dangane da warware wannan matsala, kamar kudurorin dake kunshe da daidaita tsakanin ikon kasa da zaman lafiya, shawarwarin zaman lafiya da kasashen Larabawa suka yi, shirye-shiryen shimfida zaman lafiya na gabas ta tsakiya da dai sauransu.

Bugu da kari, Sin na fatan za a iya cimma ra'ayi daya ta hanyar shawarwarin siyasa, da ke tsakanin kasashen Isra'ila da Falesdinu, ta yadda za a iya ba da taimako ga Falesdinu, domin ta samu damar gina kasarta da kanta, lamarin da zai taimaka wajen tabbatar zaman lafiya tsakanin kasashen biyu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China