in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Isra'ila da Palasdinu sun tsagaita bude wuta daga daren 21 ga wata, in ji ministan harkokin wajen Masar
2012-11-22 15:17:28 cri
Ranar 21 ga wata a birnin Alkahira, ministan harkokin waje na kasar Masar Mohammed Kamel Amr, ya sanar da cewa, Isra'ila da Palasdinu sun amince da tsagaita bude wuta daga daren ranar 21 ga wata da misali karfe tara.

Yayin taron manema labaru da aka yi a wannan rana, Mohammed Kamel Amr ya yi kira ga kasashen biyu, da su aiwatar da yarjejeniyar hana jin karar makamai yadda ya kamata. Ya jaddada cewa, Masar ta dauki alhakin dake wuyanta na shiga tsakanin bangarorin biyu, kuma kasar ta gamsu da kokarin da kungiyar AL, MDD da kuma kasashen Qatar, Turkiya da sauran su suka yi domin kalubalantar kasashen biyu da su tsagaita bude wuta.

A wannan rana da dare, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya sanar da cewa, an kawo karshen matakin soja da Isra'ila ta dauka mai taken "Pillar of Defence" haka nan kuma an aiwatar da yarjejeniyar hana jin karar makamai daga daren ranar 21 ga wata da misali karfe tara. Yana mai jaddada cewa, tsagaita bude wuta mataki ne mai amfani da Isra'ila ta dauka. Bugu da kari, an ce, Isra'ila ta yanke shawarar sassauta takunkumin da ta sanya, wajen hana mutanen da suka ratsa yankin Gaza, da kuma sufurin kayayyaki ta wannan yanki.

Babban sakataren MDD Ban Ki-Moon ya yi maraba da yarjejeniyar da kasashen biyu suka kulla, kuma ya nuna gamsuwa da kokarin da Masar ta yi a wannan fanni.

Dadin dadawa, shugaban majalisar EU Herman Van Rompuy, da shugaban kwamitin EU Manuel Durão Barroso, sun ba da haddadiyar sanarwa a wannan rana, don nuna amincewa da wannan yarjejeniya.

Haka zalika Shugaban kasar Amurka Barack Obama, ya bugawa shugaban kasar Masar Mohamed Morsy, sakamakon cimma matsaya daya ta hadin gwiwa, wajen fitar da wani tsarin magance rikicin tsaro a wannan lokaci. Ban da haka, Barack Obama ya bugawa Benjamin Netanyahu waya, inda ya bayyana yabo gare shi kan matakin da ya dauka na tsagaita bude wuta, tare kuma da nanata ikon Isra'ila na kare kanta. (Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China