in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakataren harkokin waje ta kasar Amurka ya yi kira da a farfado da shawarwarin shimfida zaman lafiya tsakanin Palasdinu da Isra'ila
2013-07-18 17:19:47 cri

Wani jigon Palasdinu ya nuna a ran 17 ga wata cewa, sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry ya gabatarwa shugaban Palasdinu Mahmoud Abbas wani shirin farfado da shawarwarin shimfida zaman lafiya tsakanin Palasdinu da Isra'ila a wannan rana, a birnin Amman hedkwatar kasar Jordan.

Mutumin Palasdinu wanda bai fayyace sunansa ba ya ce, wannan shiri zai farfado da shawarwarin daga fannoni uku wato siyasa, tsaro da kuma tattalin arziki.

Amurka ta nemi Palasdinu da Isra'ila da su mutunta shatin iyakar kasa da ke tsakaninsu kafin yakin shekarar 1967, kana ta nemi Isra'ila da ta dakatar da gina matsugunan Yahudawa. Ban da haka, Amurka ta kalubalanci Isra'ila da ta saki karin Palasdinawa da take tsare dasu. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China