in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mahmoud Abbas ya bayyana manyan batutuwa da za a tattauna kansu a zagaye na biyu na shawarwari tsakanin Palasdinu da Isra'ila
2013-08-16 15:54:55 cri

Shugaban Palasdinu Mahmoud Abbas ya nuna a ran 15 ga wata a birnin Ramallah dake yammacin gabar kogin Jordan cewa, Palasdinu da Isra'ila sun yi shawarwari a zagaye na biyu a birnin Kudus a ran 14 ga wata, inda suka tattauna dukan muhimman batutuwa tsakaninsu.

A gun taron manema labaru da ya yi tare da Ban Ki-Moon babban sakataren MDD wanda yake yin ziyara a Palesdinu, Abbas ya ce, daga cikin manyan batutuwan da suka tattauna har da matsalar tsaro, shata iyakar kasa, mallakar kan birnin Kudus da kuma maido da 'yan gudun hijira na Palasdinu. Ya jaddada cewa, yin shawarwari ita ce hanya daya tilo wajen kafa kasar Palasdinu mai cin gashin kanta. Hakan ne ya sa, Palasdinu ta nuna himma da kwazo game da shawarwarin, inda ya ce ya kamata, Isra'ila ta yi iyakacin kokari don dakatar da gina matsugunan Yahudawa da sakin 'yan Palasdinawa da take tsare da su a baya tare kuma da bayyana matsayin da ya dace a cikin shawarwarin.

A gun taron manema labaru, Ban Ki-Moon ya jinjina matakin da shugabannin Palesdinu da na Isra'ila suka dauka na komawa teburin shawarwari, kuma ya yi kira ga bangarorin biyu da kada su dauki matakan da za su kawo cikas ga shawarwarin. Ban da haka, ya nuna damuwa sosai ga matakin da Isara'ila ta dauka na gida matsugunan Yahudawa a yammacin gabar kogin Jordan da gabashin birnin Kudus, abin da zai watsar da amincewar da Palesdinawa ke nuna wa Isra'ila kan matsalar ko ta dukufa kan aikin shimfida zaman lafiya ko a'a.

Dadin dadawa, Ban Ki-Moon ya nuna farin ciki sosai ga sakin Palasdinawa 26 da Isra'ila ta yi, kuma ya nuna damuwa sosai ga wasu Palasdinawa 5000 wadanda har yanzu ake tsare da su a Isra'ila. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China