A cikin wata sanarwar da ma'aikatar harkokin waje ta kasar Jordan ta bayar a wannan rana, an ce, a yayin ganawar Judeh da Vershinin, sun yi musayar ra'ayoyi kan yadda za a sa kaimi ga samun zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya da kuma bunkasuwar yanayin da ake ciki a yankin, kuma sun jaddada cewa, za su yi kokari wajen tabbatar da ganin an kafa kasar Palesdinu mai cin gashin kanta a karkashin tsarin shirin warware rikicin a tsakanin bangarorin biyu, kuma ya kamata a sake yin shawarwari kai tsaye a tsakaninsu don cimma burin samun zaman lafiya a tsakanin bangarorin biyu. (Zainab)