Ana ci gaba da kokarin cimma matsaya tsakanin bangarorin biyu, wacce a fadin sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry a makon da ya gabata, ita ce za ta zamo tushin yin tattaunawa kai tsaye.
Kerry ya bayyana ranar juma'a Juma'a a karshen ziyararsa ta kwanaki hudu a kasar Jordan cewa idan komai ya tafi yadda ake so, mai yarjejeniya a madadin Falasdinu Saeb Erakat da takwaransa na Isra'ila Tzipi Livni zasu hadu a birnin Washington cikin 'yan makonni masu zuwa don ci gaba kan haka.
Mai Magana da yawun fadar White House Jay Carney ya ce suna kokarin sanya rana da bangarorin 2 za su je Washington nan da wasu 'yan makonni don a ci gaba.
Yayin da yake jawabi da aka saba bayarwa ga 'yan jarida ya ci gaba da cewa wannan babban kalubale ne ga Isra'ilawa da Falasdinawa da ma gwamnatocin Amurka, to amman duk da hakan ba za'a bar wannan batu ba. (Lami)