Rukunin ma'aikatan ceto na farko da gwamnatin kasar Sin ta tura ya isa filin saukar jiragen sama na Ninoy Aquino dake birnin Manila hedkwatar kasar Philipines a daren jiya Laraba 20 ga wata, ban da haka, jirgin ruwa mai aikin jiyya da ake kira "ARK PEACE OF PLA" na kasar Sin shi ma ya tashi zuwa kasar Philipines a ran 21 ga wata da tsakar rana.
Rukunin ma'aikatan ceto da Sin ta tura a wannan karo yana kunshe da mutane 18, ciki hadda masu aikin ceto, masu aikin jiyya, masu ba da hidima. Shugaban rukunin Sun Shuopeng ya bayyana cewa, za su isa birnin Tacloban inda ya fi fama da hadarin cikin sauri, domin gudanar da aikin ceto a wuri na tsawon kwanaki 15. Idan kasar Philipines ta bukaci hakan, Sin za ta ci gaba da tura masu aikin ceto da masu aikin jiyya.
A sa'i daya kuma, rukunin ma'aikatan ceto na daban karkashen jagorancin Zhao Baige, mataimakin shugaba na farko na kungiyar Red Cross ta kasar Sin ya isa kasar a yammacin yau 21 ga wata. Ban da haka, kashi na 2 na rukunin ma'aikatan ceto dake kunshe da mutane 10 da kungiyar Red Cross ta kasar Sin ta shirya zai isa kasar a ran 23 ga wata domin ba da taimakon jiyya yadda ya kamata. (Amina)