An yi wani dauki ba dadi tsakanin rundunar tsaro ta kasar Iraq da 'yan zanga-zanga mabiyan darikar Sunni a birnin Hawija, na lardin Kirkuk dake arewacin kasar Iraq, a ran 23 ga wata, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kimanin 50, yayin da wasu fiye da 150 suka samu raunuka.
Wani jami'in wurin ya bayyana cewa, rundunar tsaron kasar ta shiga sansanin kungiyar adawa ta darikar Sunni dake birnin Hawija da misalin karfe 5 da sanyin safiyar ranar Talata 23 ga watan nan, inda nan take rikici ya barke tsakaninta da 'yan darikar. Jami'in ya kara da cewa, rundunar ta tarwatsa 'yan zanga-zanga da bindigar ruwan zafi, amma 'yan zanga-zanga sun maida martani tare da bude wuta. An ce daga cikin mutanen da suka mura har da jami'an tsaro 9 na kasar Iraq.
Ma'aikatar tsaron kasar Iraq ta ba da wata sanarwa bayan aukuwar rikicin, tana mai cewa, 'yan kungiyar Al-Qaeda da wasu mambobin jam'iyyar Baath ta Larabawa, na boye tsakanin masu zanga-zangar. Amma a nasu bangare, wasu mambobin darikar Suuni sun bayyana cewa, masu zanga-zanga ba su yi harbi da farko ba, sun mayar da martani ne kawai da sanduna, da kuma duwatsu. (Amina)