in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 15 suka hallaka a wani hadarin mota a kan iyakar kasar Sudan da Libya
2013-06-03 10:38:31 cri

A kalla mutane 15 suka hallaka, sannan guda 5 suka ji rauni a kan iyakar kasar Sudan da Libya lokacin da motarsu ta kife a sanadiyar biyo su da jami'an tsaron kan iyaka suka yi, in ji ma'aikatar harkokin waje na Sudan a jiya Lahadi.

A cikin wata sanarwa, ma'aikatar ta ce, 'yan kasar Sudan din 12 da mutane uku 'yan wassu kasashe makwabta suna daga cikin wadanda suka rasa rayukansu a sanadin biyo su da jami'an tsaron kasar Libya suka yi da niyyar binciken masu safaran mutane.

An gane 7 daga cikin mamatan, sannan ana kokarin gane asalin sauran, in ji sanarwa wadda ta yi bayanin cewa, sauran wadanda suka ji rauni suna samun jinya a asibitin Al-Kufrah.

Babban ofishin jakadancin Sudan a kasar Libya sun riga sun nuna bukatarsu na son bin bahasin wannan al'amari, muhukuntar kasar Sudan sun yi bayanin cewa, za su kira jami'in diplomasiyya na kasar Libya dake Sudan domin neman karin bayani game da haka tare da bukatar a aiwatar da cikakken bincike.

Ma'aikatar harkokin waje na kasar Sudan ta gargadi jama'arta da ke ziyara a kasar Libya da su guji amfani da barauniyar hanya, sannan kada su kuskura su hada kai da masu safaran mutane, suna nunin ga cewa, akwai matukar hatsari da za su iya fuskanta a Hamada tsakanin kasashen biyu.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China