in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ofishin jakadancin Sin a San Francisco ya tabbatar da mutuwar Sinawa biyu sakamakon wani hadarin jirgin sama
2013-07-07 16:35:04 cri

Ofishin jakadancin kasar Sin dake birnin San Francisco na kasar Amurka ya tabbatar da rasuwar Sinawa guda Biyu, sakamakon faduwar da wani jirgin fasinja ya yi, yayin da yake kokarin sauka a babban filin jirgin dake birnin San Francisco da maraicen ranar Asabar 6 ga wata.

Rahotanni don gane da wannan hadari dai sun bayyana cewa, jirgin kirar Boeing 777 mallakar kamfanin Asiana na kasar Korea ta Kudu, ya tashi ne daga birnin seoul na Korea ta Kudu, kafin ya samu tangardar sauka, lamarinda ya sanya wasu sassan jikinsa karkaryewa, baya ga samansa da ya kama da wuta ya kuma kone kurmus.

Bugu da kari ofishin Asiana dake birnin seoul ya tabbatar da cewa jirgin na dauke ne da fasinjoji 291, da kuma jami'an masu kula da shi 16. mahukunta a birnin na San Francisco sun ce hadarin ba shi da alaka da harin ta'addanci. (Saminu Alhassan Usman)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China