Mai magana da yawun hedkwatar tsaro na kasar Burgediya janar Chris Olukolade ya bayyana cikin wata sanarwa da aka baiwa 'yan jarida a Abuja, babban birnin kasar, cewa jirgin yana aiki ne da bai shafi wani fada ba, lokacin da ya fado.
Jirgin saman na daga cikin guda hudu dake Niamey, wato cikin na aikin kafa zaman lafiya a kasar Mali da Afirka ke jagoranta.
Tuni dai an fara bincike don gano abin da ya haifar da aukuwar hadarin, in ji Olukolade tare da Karin cewa, za'a bada cikakken bayani da zaran an sanar da iyalan matuka jirgin. (Lami)