in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mahaukaciyar guguwa mai suna Nock-Ten ta yiwa mutane dubu 760 lardin Hainan da ke kudancin kasar Sin barna
2011-07-31 17:07:25 cri

Bisa labarin da hukumar da abin ya shafa na lardin Hainan da ke kudancin kasar Sin ta bayar, an ce, mahaukaciyar guguwa mai suna Nock-Ten ta yi barna ga gundumomi da birane 12, mutane dubu 756.2 ne su yi fama da bala'in, kuma mutane 2 sun mutu, yawan dukiyar da mahaukaciyar guguwa ta lalata ya kai RMB miliyan 377.

A ran 29 ga wata da dare, mahaukaciyar guguwa mai suna Nock-Ten ta isa yankin arewa maso gabashin lardin Hainan, kuma karfinta ya kai digiri 10. Kuma tana dauke da ruwan sama sosai lamarin da ya haddasa bala'in.

Bisa labarin da cibiyar nazarin yanayi ta lardin Guangdong ta bayar, an ce, a ran 30 ga wata da yamma, mahaukaciyar guguwa mai suna Nock-Ten ta nufi tekun Gulf Beibu alamarin da ya kai ga raguwar barazanar bala'in.(Abubakar)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China