in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane fiye da 60 sun mutu sakamakon fashewar da aka yi a wata ma'aikatar yin takin zamani ta Amurka
2013-04-18 16:43:47 cri

An samu fashewa a wata ma'aikatar yin takin zamani a jihar Texas ta kasar Amurka a ran 17 ga wata, lamarin da ya hadasa mutuwar mutane fiye da 60 yayin da darurruwan mutane suka raunana.

Kafar yada labaru ta wurin ta ba da labari cewa, hadarin ya abku ne a ranar 17 ga wata da magariba, baya ga asarar rayuka da raunata jama'a fiye da dari, kuma gine-gine wajen goma ne wutar ta lakume. A halin yanzu an janye mazaunan dake kewaye wannan wuri, kuma hukumomin kasar sun tura jiragen saman ba da agaji shida zuwa inda wannan bala'I ya abku domin taimakawa masu aikin ceto.

Har ila yau, ba a san hakikanin abubuwan da suka hadasa hadari ba tukuna. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China