in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hadarin jirgin ruwa ya hallaka sama da mutane 50 a Nigeria
2013-03-21 10:01:39 cri

Wani jirgin ruwa makare da mutane da ya nutse ranar Talatar da ta gabata a gabar tekun jihar Cross Rivers dake kudancin Nigeria, ya sabbaba mutuwar mutane sama da 50.

A cewar wadanda suka ganewa idonsu aukuwar lamarin, an cika jirgin da fasinjojin da suka wuce kima, lamarin da ya sanya shi karyewa, ya kuma nutse da mutane sama da 160 dake cikinsa, jim kadan da barin sa tashar garin Calabar.

Rahotanni dai sun nuna cewa, an shiga aikin ceton mutanen da suke cikin jirgin yayin da hadarin ya auku, sai dai ya zuwa ranar Laraba, an tabbatar da mutuwar da dama daga cikin su.

Da take tsokaci kan lamarin, mai magana da yawun kungiyar ba da agaji ta Red Cross ta nahiyar Afirka Katherine Mueller, ta bayyana wa kamfanin dillacin labaran kasar Sin Xinhua cewa, suna ci gaba da tattara bayanai kan aukuwar wannan lamari. Shi ma a nasa bangare, kakakin hukumar ba da agajin gaggawa ta Nigeria NEMA Yusha'u Shuaib, cewa ya yi, ya zuwa daren ranar Talata, an gano mutane biyu da ransu, tare da wasu gawawwakin mutane 9, ko da yake wata majiya daga asibitin da aka kai gawawwakin ta ce, yawan mutanen da suka rasu ya haura wannan adadi.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China