A ranar Talata, mahukuntan rundunar sojin saman Najeriya suka gano matuka jirgin sama biyu da suka mutu bayan da jirgin da suke ciki ya fado a Niamey, babban birnin jamhuriyar Nijar a ranar Litinin.
A cikin wata sanarwa, mai magana da yawun rundunar sojin sama ta Najeriya Air Commodore Yusuf Anas ya bayyana cewa, Benjamin Ado, wanda shugaba ne na shiyya da Ayuba Layelmenson, wanda jami'i ne na tuki, su ne suka mutu a hatsarin.
A fadinsa, jami'an biyu suna aiki ne tare da rundunar sojin sama karkashin hukumar kafa zaman lafiya ta kasa da kasa a kasar Mali karkashin jagorancin Afirka, (AFISMA) dake da sansani a Niamey.
An fara binciken musababbin hatsarin jirgin da ya fado ranar Litinin yayin da yake kan aiki da bai shafi fada ba, in ji rundunar sojin Najeriyan.(Lami)