Wen Jiabao ya ce, kamata ya yi a mai da hankali sosai game da ambaliyar ruwa da mahaukaciyar guguwa za ta kawo wa kogunan Chang Jiang da Huang He da Huai He, da kuma tabkin Tai Hu, kamata ya yi in ji Mr. Wen a hada aikin yaki da ambaliyar ruwa da magance mahaukaciyar guguwar iska tare. Ban da wannan kuma, ya zama wajibi sassan da abin ya shafa su inganta aikin sa ido game da hasashen yanayi, don shiryawa sosai wajen ceton mutane da kuma tinkarar bala'i, da mayar da aikin ceton mutane a gaban kome, kana da kara sa kulawa game da aikin yaki da ambaliyar ruwa, da kokari wajen yin rigakafin bala'in ambaliyar ruwa a duwatsu da zaizayewar kasar.(Bako)