in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutanen Sin sama da miliyan 6 suna fuskantar mahaukaciyar guguwa ta Haikui
2012-08-09 20:44:36 cri
A yau Alhamis ranar 9 ga wata, babbar hukumar ba da umurni kan yaki da ambaliyar ruwa ta kasar Sin ta ba da labari cewa, ya zuwa safiyar yau ranar 9 ga wata , mutane sama da miliyan 6 a lardunan Zhejiang, Jiangsu, Anhui, da kuma birnin Shanghai na kasar Sin sun fuskanci mahaukaciyar guguwa ta Haikui, kuma gidaje guda 7,561 sun lalace sannan kuma guguwar ta lalata amfanin gona da murabba'insu ya kai fiye da hektoci dari 3 da 380. A birnin Shanghai, mutane 2 ne suka mutu a sakamakon faduwar wani kaya daga sama da rushewar gine gine yayin da wasu 7 suka ji rauni. A lardin Anhui kuma, mutum daya ya mutu a sakamakon rushewar katanga a yayin da yake tsabtace hanyar magudanar ruwa.

Saidai kuma a wannan ranar da misalin karfe 12 na rana, karfin mahaukaciyar guguwa ta Haikui ta ragu inda cibiyarta ya kasance a birnin Chizhou na lardin Anhui. Saurin iska dake kusa da cibiyar ya kai matsayi na 7. An yi kiyasin cewa, a kwanaki biyu masu zuwa, mahaukaciyar guguwa ta Haikui za ta doshi kudancin lardin Anhui tare da raguwan karfinta. Kawo yanzu dai, ruwan koguna dake lardin Zhejiang ya riga ya ragu, sai dai ruwan kogin Shuiyang na lardin Anhui da na kogin Qinhuai na lardin Jiangsu na ci gaba da hauhawa. (Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China