Jami'in ya nuna cewa, mai yiwuwa rashin kyawun yanayin a daren ne babban dalilin da ya sa jirgin ruwan ya kife, bayan tasowar iska mai karfi gami da babbar igiyar ruwa. Ya ci gaba da cewa, ya zuwa yanzu, an tsinto gawawwakin guda arba'in da uku na wadanda hadarin ya rutsa da su, amma ba a iya tabbatar da asalinsu ba.
Wani 'dan kasar Burkina Faso da ya tsira da ransa daga hadarin ya yi bayanin cewa, jirgin ruwan ya taso ne daga kasar Nijeriya kwanaki huda da suka gabata, kafin ya gamu da hadarin, kuma mafi yawan wadanda suke cikin jirgin ruwan 'yan kasashen Burkina Faso, Benin, Nijeriya da kuma wasu kasashen yammacin Afirka ne. (Maryam)