in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenyatta ya lashi takobin daukar kwararan matakan kare hadurran mota a Kenya
2013-08-30 10:54:07 cri

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta, ya lashi takobin daukar kwararan matakan kare hadurran mota a dukkanin titunan dake fadin kasarsa, bayan da wasu mutane 41 suka rasa rayukansu, kana wasu 33 suka jikkata, lokacin da wata motar safa dake dauke da su ta kife a garin Narok kusa da Nairobi, babban birnin kasar.

Shugaba Kenyatta wanda ya gabatar da sakon ta'aziyyarsa ga iyalan wadanda suka rasu a sakamakon aukuwar hadarin na ranar Alhamis, ya ce, gwamnati ba za ta laminci asarar rayukan bayin Allah sakamakon tukin ganganci da wasu direbobi ke yi ba, yana mai cewa, wajibi ne masu motocin haya su rika sanya ido kan yadda direbobinsu ke gudanar da sana'ar tuki, baya ga batun samun kudaden shiga.

Motar kirar safa wadda ta kwace daga titi, ta kuma fada rami na kan hanyarta ne ta zuwa yammacin kasar daga birnin Nairobi.

Wani jami'in kula da dokokin hanya, Samuel Kimaru ya ce, hadarin na da nasaba da tukin ganganci da direban motar ke yi lokacin da lamarin ya auku. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China