in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 37 ne suka mutu a gabashin kasar Indiya sakamakon hadarin jirgin kasa
2013-08-19 20:48:25 cri
Wani babban jami'in 'yan sanda a kasar Indiya ya fada a ranar Litinin cewa, mutane 37 ne ciki har da mata da kananan yara suka mutu,yayin da sama da mutane 70 suka jikkata bayan da wani jirgin kasa da ke sheka gudu ya bi ta kansu a wata tashar jirgin kasa da ke kauyen jihar Bihar da ke gabashin kasar Indiya.

Lamarin ya faru ne lokacin da wadanda hadarin ya rusa da su galibin su 'yan Hindu masu ziyarar Ibada ke kan hanyar su ta zuwa wani wurin baje kolin kayayyaki ke kokarin ketare titin layin dogo a tashar jirgin kasan karkarar Dhamara,kimanin kilomita 200 daga Patna babban birnin jihar,inda jirgin da ke sheka gudu ya murkushe su ya kuma halaka mutane 37 nan take kana ya jikkata wasu 70, inda aka kwantar da su a wani asibiti da ke kusa,yayin da wasu kuma suka ji rauni mai tsanani.

Wani jami'in da ya bukaci a boye sunansa ya ce, adadin wadanda suka mutu yana iya karuwa. Kuma jami'an kula da jiragen kasa na kasar Indiya sun bayyana cewa,jirgin da ke sheka gudu, bai rage gudu ba a lokacin da ya doshi tashar,domin ba a tsara cewa jirgin zai tsaya a tashar ba tun farko.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China