An ce, don tinkarar wadannan mahaukatan guguwai guda 2, a ranar 31 ga watan Yuli, ofishin kula da aukuwar bala'u na kasar Sin ya kaddamar da tsarin daukan mataki game da gargadin da aka bayar, tare da shiri sosai cikin gaggawa.
A nasu bangare, gwamnatocin lardunan da guguwan suka shafa kamarsu Jiangsu, Zhejiang, Fujian, da Shandong sun tura kungiyoyin musamman zuwa wuraren da bala'in zai fi ritsawa da su, don ba da taimako. Kana sun yi kokarin samar da kayayyakin da ake bukata kamarsu tantuna, barguna, tawulan goge jiki, don tallafa wa jama'ar da aka riga aka kawar. (Bello Wang)