in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ofishin jakadancin kasar Sin dake Amurka ya dufuka kan aikin daidaita hadarin jirgen saman da ya faru a birnin San Francisco
2013-07-08 16:36:05 cri

Bayan abkuwar hadarin jirgen saman kamfanin Asiana na Korea ta kudu a filin saukar jiragen sama na San Francisco na kasar Amurka a ran 6 ga wata, wanda ya yi sanadiyyar asarar rayuka da raunukan Sinawa, nan da nan ofishin karamin jakadan kasar Sin dake birnin San Francisco ya kafa wani kwamitin dake karkashin jagorancin babban kansula Yuan Nansheng domin kula da halin ko ta kwana, wanda ya tuntubi bangarorin da abin ya shafa tare kuma da yin tattaki zuwa filin saukar jiragen sama da kuma asibiti ba da jimawa ba.

A sa'i daya kuma, jakadan kasar Sin dake Amurka Cui Tiankai ya bugawa mataimakiyar sakataren harkokin waje na kasar Amurka Wendy Sherman a ran 6 ga wata domin jaddada muhimmancin da gwamnatin kasar Sin ta dora kan wannan lamari, tare da fatan Amurka za ta yi bincike kan lamarin nan da nan da gudanar da aikin ceto yadda ya kamata.

Madam Wendy Sherman da sauran jami'an Amurka sun nuna juyayi sosai ga Sinawan da suka rasa rayukansu a cikin wannan hadari, tare kuma da jajantawa wadanda suka ji rauni, tana mai cewa, Amurka za ta yi iyakacin kokarin baiwa iyalan mamata na kasar Sin taimako. Jakadan kasar Korea ta kudu ya nuna cewa, Korea ta kudu za ta ci gaba da baiwa kasar Sin duk wani taimakon da ya wajaba. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China