Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin dake MDD Wang Min ya bayyana a ran 21 ga wata cewa, tallafawa kasashe mafi koma bayan tattalin arziki da kasashe maso tasowa da ba su kusa da teku wajen samun ci gabansu na da muhimmiyar ma'ana ta fannin cimma muradun karni na MDD da bunkasuwar tattalin arzikin duniya, ya kamata, kasashen duniya cika alkawarin da suka yi na ba da taimako ga kasashen.
A gun taron da kwamiti na biyu mai kula da harkokin tattalin arziki na babban taron MDD ya kira wanda ke da jigon "kasashen dake fuskantar mawuyacin hali", Wang Min ya nuna cewa, Sin ta kan tsaya tsayin daka kan matsayin gayon bayan raya kasashen mafi koma bayan tattalin arziki da kasashe maso tasowa da ba kusa da teku ba, kuma tana kokarin taka rawarsa gwargwadon karfinta ta hanyoyi daban-daban bisa tsarin hadin kai tsakanin kasashen maso tasowa. Ban da haka, Sin ta yi alkawarin cire harajin kwastan kashi 97 bisa dari na hajjojin da take shigowa daga kasashe mafi koma bayan tattalin arziki da suka kulla dangantakar diplomasiyya tsakaninta da Sin. Sin za ta ci gaba da ba da taimakonta ga wadannan kasashe gwargwadon karfinta. (Amina)