Wata sanarwa data fito da ofishin kakakinsa, tace tuni Mr. Ban, ya zanta da shugaba Uhuru Kenyatta ta wayar tarho, ya kuma gabatar da sakon ta'aziyyarsa ga iyalai, da 'yan uwan wadanda suka rasa rayukansu, da wadanda suka jikkata.
Bugu da kari babban magatakardar MDDr ya yi imanin cewa bada wani bata loakci ba, da a kai ga hukunta wadanda suka aikata wannan laifi.
A wani labarin kuma mai alaka da wannan, mambobin kwamitin sulhun MDDr sun fidda wata sanarwa dake tir da aukuwar wannan hari, suna masu jaddada aniyarsu ta goyon bayan dukkanin wani mataki da zai kawo karshen ayyukan ta'addanci a dukkanin fadin duniya.
Wannan dai harin da wasu dakaru dauke da makamai suka kai a wata cibiyar kasuwanci dake birnin na Nairobi, a ranar Asabar 21 ga wata, ya sabbaba rasuwar mutane da dama, baya ga wasu karin mutane da 'yan bindigar suka yi garkuwa da su. (Saminu Alhassan Usman)