Babban magatakardan majalisar Ban Ki-Moon ne ya gabatar da sabuwar rahoton da ke nuna cewa duk da nasarorin da aka samu rikicin tattalin arziki na duniya na cigaba da kawo cikas ga ayyukan cimma burin muradun karni.
A lokacin bayaninsa ya shaida ma manema labarai cewa sabbin kasashe da sauran abokan hadin gwiwa suna yunkurowa amma duk da hakan wajibi ne kowa ya kara himma a kan taimaka ma ayyukan cigaba a hukumance, yanayin kudi da samar da ababen bukatun cikin gida.
A karkashin taken Hadin gwiwwar duniya don cigaba;kalubalen da muke fuskanta, rahoton yace dole ne kasashen duniya su sake kara himma wajen bada taimako tare da cimma wata yarjejeniya a kan hada hadar kasuwancin da zai kawo cigaba ta fannoni da dama.(Fatimah Jibril)