in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rukunin bincike na MDD kan makamai masu guba na kasar Syria ya koma kasar Syria
2013-09-25 20:28:46 cri
A ranar 25 ga wata da tsakar rana, rukunin bincike na MDD kan makamai masu guba na kasar Syria ya isa birnin Damascus don ci gaba da yin bincike kan zargin yin amfani da makamai masu guba a kasar.

A wannan karo, rukunin ya kunshi membobi fiye da 10, ciki har da shugaban rukunin Ake Sellstrom, wato kasa da adadin karon da ya gabata.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, rukunin zai ci gaba da yin bincike kan zargin yin amfani da makamai masu guba a kasar, ciki har da lamarin kai hari da makamai masu guba a Khan al-Asal dake jihar Aleppo ta kasar a ranar 19 ga watan Maris na bana. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China