in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta ci gaba da shiga aikin tattara kudi game da raya kasashen duniya
2013-10-08 11:11:12 cri

Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin dake MDD Wang Min ya nuna a ran 7 ga wata a gun taron manyan jami'ai dake tattauna batun tattara kudin samun bunkasuwa karo na shida na MDD cewa, Sin kasa ce dake kokarin tafiyar da wannan aiki, kuma za ta ci gaba da ba da gudunmawa a wannan fanni.

A cikin jawabinsa, Wang Min ya furta cewa, Sin ta ba da taimakonta ga sauran kasashe masu tasowa gwargwadon karfinta yayin da take neman samun bunkasuwar kanta. Ban da haka, Sin ta cika dukkan alkawuran da ta dauka wajen ba da taimako ga sauran kasashe maso tasowa, ciki hadda kyautata zaman rayuwar jama'a, rage basusuka, kara ba da horaswa a fannin hada-hadar kudi, tattalin arziki da ciniki, sha'anin noma, kwadago da sauransu.

Wang Min yana mai cewa, Sin za ta ci gaba da shiga aikin tattara kudin raya duniya nan gaba, tare kuma da sa kaimi ga tabbatar da yarjejeniyar Monterrey da sanarwar tattara kudi ta Doha, har ma da ba da gudunmawa wajen samun bunkasuwa da hada kan kasa da kasa. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China