Liu Jieyi ya nuna cewa, a halin yanzu, ana samun canje-canje da dama a fadin duniya, ya kamata kasashen duniya su hada kai don cimma burin samun zaman lafiya, ci gaba, hadin gwiwa da cimma moriyar juna, warware matsalolin kasa da kasa da kuma fuskantar kalubaloli tare. Bugu da kari, ya kamata MDD ta ba da muhimmin taimako kan wadannan fannonin da aka ambata a matsayin kungiyar duniya wanda ta fi samun amincewa tsakannin gwamnatocin kasa da kasa.
Ya kuma kara da cewa, a matsayin zaunanniyar mambar MDD kuma babbar kasa mai tasowa, kasar Sin za ta ci gaba da nuna goyon bayanta ga MDD da kuma ayyukan bunkasuwar kasa da kasa, bugu da kari, za ta ci gaba da kare manufofi da kuma ka'idojin Kundin Tsarin mulkin MDD, kana za ta gudanar da ayyukanta yadda ya kamata cikin MDD. (Maryam)