Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin da ke MDD Mista Wang Min ya jaddada a ran 7 ga wata cewa, ya kamata MDD ta jagoranci hadin kan kasa da kasa wajen yaki da ta'addanci, tare kuma da bin dokokin duniya da kowa zai amince da shi ciki har da babban kundin mulkin MDD.
A wannan ranan, da yake jawabi a wani taro kan matakai da za a dauka domin kawar da ta'addanci a duniya da kwamiti na 6 da ke kula da harkokin dokoki na babban taro na 68 na MDD ya shirya, Mista Wang Min ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin ta nuna goyon bayan ga hukumomin da abin ya shafa da su bi hakkinsu, su kara samun sulhuntawa da hadin kansu,.
Haka kuma inji shi kasar Sin ta nuna goyon baya ga tabbatar da 'manyan tsare-tsare domin yaki da ta'addanci a duniya' yadda ya kamata, dalilin da yasa Kasar take kira ga kasa da kasa da su shiga cikin yarjejeniyoyi 13 na MDD domin yaki da ta'addanci, kuma mambobinsu su dauki nauyin da ke biya wuyansu. (Danladi)