A ranar Talata 15 ga wata ne, aka kawo karshen sabon zagaye na shawarwari a rana ta farko kan matsalar nukiliya ta kasar Iran.
Bisa labarin da muka samu, an ce, wakilin shawarwari na Iran, kuma ministan harkokin wajen kasar Mohammad-Javad Zarif ya yi bayani kan shirin kasarsa a wannan rana da safe, bayan haka bangarori daban daban da suka halarci shawarwarin sun yi nazari kan cikakkun bayanai game da shirin nukiliyar kasar ta Iran.
Michael Mann, kakakin Catherine Ashton babbar wakiliyar kungiyar EU mai kula da harkokin diplomasiyya da manufofin tsaro ya bayyana a cikin wata sanarwa bayan shawarwarin cewa, bangarorin sun tattauna sosai a wannan rana da yamma, wannan shi ne karo na farko da aka yi haka. A ran 15 ga wata da safe, bisa jagorancin Ashton, wakilan kassahen Amurka da Britaniya da Faransa da Rasha da Sin da kuma Jamus tare da wakilan Iran sun isa fadar 'palace of nations' wato ofishin MDD da ke birnin Geneva, inda suka fara yin shawarwari da za a shafe kwanaki biyu ana yinsa.(Danladi)