Babban sakataren MDD Ban Ki-moon, shugaban babban taron MDD karo na 68 John William Ashe da wasu jami'an harkokin wajen kasashen duniya sun halarci bikin da aka yi a wannan rana da safe, kuma, Mr. Ban Ki-moon ya kada babbar kararrawar zaman lafiya.
Yayin da Ban Ki moon ke ba da jawabi a wannan biki, ya bayanna cewa, ranar zaman lafiyar kasa da kasa lokaci ne da za a tuna tarihi, jaddada niyyar hana yake-yake da kuma yin kira ga kasa da kasa da su dakatar da aikace-aikacen tashin hankali. Mr. Ban ya kuma yi kira ga al'ummar kasa da kasa da su yi shiru na minti daya da tsakar rana agogon wuraren su, don tuna wadanda suka rasa rayukansu cikin rikice-rikice, da kuma wadanda suka tsira daga rikice-rikice.
Babban taken ranar zaman lafiya ta shekarar bana shi ne, "inganta zaman lafiyar kasa da kasa ta hanyar raya ayyukan ba da ilmi". Yayin da ya ke ba da jawabi, Mr. Ban ya nuna cewa, aikin ba da ilmi na da muhimmiyar ma'ana wajen kyautata halayan jama'ar kasa da kasa da kuma kiyaye zaman lafiyar zaman takewar al'umma. (Maryam)