in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Saudiya ta ki karban kujeran mamban kwamitin tsaro na MDD
2013-10-18 21:05:22 cri
Rahotanni daga Riyadh, fadar gwamnatin kasar Saudiya, a ranar Jumma'ar nan 18 ga wata na nuna cewar, kasar ta ki karbar kujerar kwamitin tsaro na karba-karba da MDD ta ba ta domin nuna rashin jin dadinta game da rawar da kwamitin ta taka wajen duba batutuwan da suka shafi yankin Gabas ta Tsakiya.

A cikiin wata sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen kasar Saudiya ta fitar kuma kamfanin dillancin labarai na kasar ta ruwaito, an ce, kasar ta bayyana gazawar kwamitin wajen warware batun kasar Syria da kuma bukatar Palasdinu sannan kuma da kin mai da yankin Gabas ta Tsakiya wani yankin da ba shi da sauran makaman kare dangi a cikin dalilan da suka sa ba za ta karbi wannan kujera ba.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China