Sakataren gudanarwar yarjejeniyar Mr. Gnacadja ya bayyana cewa, kasashe daban-daban da wannan batu ya shafa sun amince da kafa wani wamiti tsakanin gwamnatocinsu, domin cimma burin da aka gabatar a babban taron samun bunkasuwa mai dorewa na MDD, na tabbatar da rashin yaduwar hamada.
Wannan kwamiti a cewarsa zai ba da damar ci gaba da nazarin matsalar kwararowar hamada, tare da gabatar da matakan da za a dauka. Ban da haka, bangarorin sun kuma gabatar da shawarwarin da suka shafi yadda za a gudanar da yarjejeniyar. Dadin dadawa, taron ya zartas da wani bayani daya shafi kasafin kudi Euro miliyan 16.1, wanda za a yi amfani da shi cikin shekaru biyu masu zuwa.
Taron ya samu mahalarta kimanin 3000, ciki hadda ministoci 45. (Amina)