Rahotanni daga mahukuntan kasar Sin sun tabbatar da cewa, ministan harkokin wajen kasar Sin Mista Wang Yi, zai halarci muhawarar da za a gudanar, inda zai gabatar da manufar sabuwar gwamnatin kasar Sin a fannin harkokin diplomasiya.
Ana sa ran halartar ministocin kasashe 193, masu kujeru a MDD a wannan karo.
Ban da babbar muhawarar da wasu tarukan manyan jami'ai, za kuma a shirya ganawa da tattaunawa tsakanin bangarori daban daban. Game da taron na bana, wata majiya a fannin harkar diplomasiya ta ce, ana sa ran ganin fuskokin shuwagabannin kasashe fiye da 140.
Wani abin lura shi ne akwai sabbin fuskokin da za su bayyana a taron na wannan karo, domin ban da minista Wang Yi na kasar Sin da zai halarci bikin a karon farko, shi ma shugaban kasar Iran Hassan Rohani, na cikin sabbin fuskokin da ake fatan za su bayyana.
Tuni dai sabuwar manufar kasar ta Iran, da shugaba Rohani ya bayyana dake kunshe da aniyar kauracewa samar da makaman kare-dangi, ta sanya huldar dake tsakanin Iran da Amurka ta fara kyautatuwa, don haka ne ma ake hasashen yiwuwar gamuwar shugabannin kasashen 2 a wajen babban taron MDDr na wannan lokaci.
Game da hakan tuni fadar shugaban Amurka White House ta riga ta bayyana cewa, shugaba Obama ba shi da shirin ganawa da Rohani, ko da yake yanayin gudanar taron na iya hada fuskokin shuwagabannin biyu. (Bello Wang)